Main menu

Pages

'Ni kadai ce 'yar jarida a garinmu'

Maryan Seylac dai 'yar jarida ce daga kasar Somaliya. Ta na daya daga cikin mata masu daukar rahoto daga jihar da ta fito wato Baidoa, kuma ta kafa wata kungiya da ta ke karfafawa mata 'yan jarida gwiwa a kasar.

Ta shaida wa BBC cewa tarihin rayuwarta, ciki har da kalubalen da mata kan fuskanta a daya daga cikin kasashe masu matukar hadari ga 'yan jarida. Akwai lokacin da kiris ya rage masu tada kayar baya na kungiyar al-Shabab su hallakata.
Presentational grey line
Tun ina karama na ke sha'awar aikin jarida, ina yawan sauraron labaran sashen Somali na BBC tare da mahaifina, mu kan kuma tattauna labaran da muka saurara da shi. Ta haka ne sha'awar aikin jarida ta shiga zuciya ta kwarai da gaske.
Kasar Somalia cike ta ke da batutuwan siyasa, kuma kungiyoyi daban-daban sun yi ta yaki kan hakan tun bayan hambarar da gwamnatin soji a shekarar 1991, a lokacin shekara ta hudu a duniya.
Amma a shekarar 2012 sai lamura suka fara daidaita, amma har yanzu kasar Somaliya na da matukar hadari ga 'yan jarida, musamman idan ke mace ce.
A lokacin da muke makaranta ba na iya magana a cikin aji, ina kuma yawan tsayawa gaban dalibai kamar ina koyar da su darasi.
A kasar Somaliya iyayenmu ba sa tambayarmu abin da ka ke so ka zama idan ka kammala karatu, saboda a matsayinki na 'ya mace rayuwarki baki daya a gida ta ke karewa, daga wanki, sai girki, kula da yara da sauransu.
Amma tun ina karama na san abin da na ke son zama, wato 'yar jarida.
'Na zama abar sha'awa a bangaren watsa labarai'
Mahaifina malamin makaranta ne, kuma burinsa shi ne daya daga cikin 'ya'yansa ya gaje shi.
Saboda yayyena maza da mata ba su maida hankali dan cikar burinsa ba. A tunanin shi ni ce wadda zan bi sahun sa ta fuskar zama malamar makaranta, na kuma cika masa burin amma na dan lokaci.
Lokacin da na kammala karatun sakandare na yi koyarwa na tsawon shekara daya a Baidoa, amma fa ba shi ne aikin da na ke son yi ba.
Abokin mijina ya na aiki a gidan rediyon da ke garinmu, wata rana na tambaye shi ko zai iya sama min gurbin sanin makamar aiki a inda yake aiki ko da kuwa da yammaci ne.
Yawancin gidajen jarida da kafafen watsa labarai a Somaliya masu zaman kansu ne, sannan su na fadi tashin ganin sun gudanar da aikin da adalci, to amma fa rediyo ne babbar hanyar watsa labarai.
A matsayi na na mace tilo a wannan fanni, na zama abar sha'awa dan haka ma suka amince su ba ni horo a bangaren da na ke so.
A wasu lokutan na kan taimaka da karbar baki, kai har da karanta labarai.
Sannu a hankali sai na watsar da aikin koyarwa, na samu gurbin aiki da gidan Rrediyon da na ke yiwa aikin wuce gadi inda suka dauke ni cikakkiyar ma'aikacciya.
Sai dai 'yan uwana ba su yi murna da wannan aikin da na samu ba.
Mahaifina ya nuna damuwa matuka har ya fara hasashen da kaina zan bar aikin na zo kuma na tsugna babu wani akin yi.
Amma a kullum ina fada ma sa ''Ba na jin dadin aikin koyarwa da na ke yi. Aikin jarida shi ne burina''.
 A hankali sai mahaifina da 'yan uwana suka amince da zabi na, ganin yadda na ke jin dadin aikin nawa.
Amma lamarin babu sauki ta bangaren mutanen yankinmu, su na min kallon kaskanci tare da tuhumata kan aikin da na ke yi.
Abin ya sanya ina jin babu dadi saboda bisa al'ada mata a Somaliya abin da aka san su da shi shi ne zaman aure da bautawa miji.
Allah cikin ikonsa sai ya kasance mijina dan jarida ne da ya fahimce ni tare taimaka min wajen cimma burina. Na tabbatar da ba dan jarida na aura ba da tuni ina kulle a cikin gida.

Comments

Featured Post

Yadda Zaka Chanja Bayananka Na BVN

table of contents title