DORA Windows 7 AKAN COMPUTER
Hanyar dora Windows 7, akan computer akwai hanyoyi
1. SAKA WINDOWS 7 TA BOOTABLE CD
Wannan hanyar itace hanyar da ake iya dora Windows 7 akan computer, ta hanyar amfani da bootable CD, Idan kana da wannan bootable CD saika bi wadannan matakan, domin dora Windows akan computer dinka, Laptop, ko Desktop, saika bi wadannan matakan.
1. Kasa Windows 7 bootable CD acikin gidan saka CD na jikin computer dinka, idan kuma baka da shi, ko kuma naka baya aiki, kana iya amfani da CD na waje (External CD ROM), idan kasa shi, saika latsa My Computer domin ka tabbatar CD daka sa ya hau, idan ka tabbatar ya hau shi kenan.
2. Saika yi mata reboot, wato ka latsa Windows Start Menu >Switch Option sannan ka latsa Reboot. Abinda ake the bukata anan shi ne ka lura da tana tafiya reboot.
3. Tana reboot yayinda take kokarin dawowa, saikai sauri ka danna F9 , ko F12, ko F7 ko ka latsa madannin C, ya danganta da yanayin tsarin boot Option na computer dinka. wanda ya latsa F7, ko F12,ko F9 akwai bukatar ya zabi CD ROM, domin cewar yana bukatar na'urarsa ta tashi daga CD ROOM.
6. Zata baka wannan allon
4. Kana zabar CD ROM zata baka bakin allo da cewar “Press any key to boot from a CD or DVD.._"
kayi sauri ka latsa ko wane irin madanni ajikin keyboard dinka kafin wannan bakin allon ya kauce, idan wannan rubutun ya kauce, saika sake mai-maita mataki na biyu dana uku.
5. Yayin daka danna kowanne irin madanni, ko kafin ka latsa tana iya baka wannan allon,
5. Yayin daka danna kowanne irin madanni, ko kafin ka latsa tana iya baka wannan allon,
Idan ta baka wannan allon, saika latsa madannin "Enter" domin bukatarka ta dora Windows 7 akan pc dinka. shi wannan allon yana iya zuwa kafin mataki na hudu ma, wato kana zabar CD ROM boot,tana iya baka wannan allon a matakinka na gaba
6. Zata baka wannan allon
da cewar "Windows is loading files...
." anan ba'a bukatar ka latsa komai.
7. Zata baka allo na gaba, ka zabi yaren da kake bukata Windows dinka ya sauka da shi, "Language to install" sannan ka zabi tsarin madannai "Keyboard
8. Bayan ta gama, allo na gaba zata baka wannan
da cewar "Install now" saika latsa "Install now"
9. Bayan ya gama, allo na gaba zai baka wanda anan zaka zabi salon saukar Windows dinka, wato Upgrade zaka yi ko kuma Custom (Advanced) to anan saika zabi advance, tunda magana muke ta dora windows da CD/DVD.
10. Anan saika latsa yar akwatin dake kasan gargadi, da kuma yarjejiniya Accept the license agree.
11. Anan ya danganta da yadda Windows dinka yake, wato wani CD/DVD Windows daya ne acikinsa, wani kuma haduwar windows ne acikinsa, idan naka ya kasance yana dauke dasu kala-kala.
12. Bayan zabar kalar Windows din da kake bukata saika yi partition wato raba hard disk dinka gida biyu. Sannan ka zabi inda kake son ka saukar da Windows dinka. Saika latsa Next
13. Nan take zai fara copy na files yana saukar dasu kan computer dinka, anan ba'a bukatar ka latsa komai. Ka jira zata bukaci tayi restart, sannan ta dawo ta karisa saukar da windows dinka, bayan ta gama da wannan matakin kana iya cire window cd dinka, ta gama saukar da shi, saura ta gyara masa zama da tsara shi.
13. Nan take zai fara copy na files yana saukar dasu kan computer dinka, anan ba'a bukatar ka latsa komai. Ka jira zata bukaci tayi restart, sannan ta dawo ta karisa saukar da windows dinka, bayan ta gama da wannan matakin kana iya cire window cd dinka, ta gama saukar da shi, saura ta gyara masa zama da tsara shi.
14. Zaka shigar da sunan da kake son amfani dashi akan ita wannan computer, sannan ka bata suna.
15. Sannan zaka shigar da lambobin mallaka wadanda suke tabbatar da ingancin windows din da kasa wato product key, lambobi ne, hade da harufa, ana iya samunsu acikin kwalin Windows CD/dvd.
16. Saika saita agogo da kwanan wata, bayan ka zabi nahiyarka, ko kasarka.
17. Saika zabi recommending settings a allo na gaba, aikinka ya kammala. Saika more lokaci da windows 7 dinka.
Comments
Post a Comment