A har kullum hanyoyin fasahohin zamani sai kara saukaka suke yi, musamman in a kayi la’akari da yadda komai yake kasancewa a sawwake sabili da mayar da shi akan wayoyin mu na hannu.
Irin wadannan hanyoyi da aka saukaka sun hada da amfani da wayar hannu wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci tsakanin bankuna, remote na Tv ko na Radio, tura sakonni na murya kona hotuna, sanya ido akan gidanka ko shagonka ta amfani da CCTV Camera, bin diddiki(tracking) da dai sauran abubuwa da dama.
Idan kun kasance kuna yawan amfani da manya-manyan akwatunan magana(Speakers) na zamani, ya’alla wajen wa’azi, a guraren Ibada, ya zuwa gidajen shakatawa, zaku fahimci cewa wataran kukan iya fuskantar matsala wajen amfani dasu wadannan akwatunan magana. Daga ciki kuwa zaku iya fuskantar daukewar abun magana wato makirfan (microphone) wacce ke isar da magana zuwa akwatun maganar.
Yadda Zaka Mayar Da Wayar taka Microphone
Daga nan sai ka kunna Bluetooth din wayar taka da kuma na speaker din da kake son ka hada su.
Bayan ka hadasu (bayan kayi connecting), sai kawai ka bude wannan manhaja (microphone ) daka dauko, inda zaka ga hoton abun magana(microphone), sai kawai ka danna shi.
Da zarar ka taba hoton mic din sai kawai ka kanga wayarka wajen bakinka sai ka cigaba da duk maganar da zakayi.
Wannan shine dan takaitaccen bayani kan yaddda zaka yi amfani da wayarka a matsayin microphone.
Zaku iya sauke wannan manhaja ta microphone ya zuwa kan wayarku kai tsaye daga nan gurin.
Comments
Post a Comment