Main menu

Pages

Barayin 'yan mata shida 'na neman kudin fansa'

A
Mutanen da suka yi garkuwa da 'yan matan sakandare shida da malamansu guda biyu a jihar Kaduna sun nemi a ba su kudin fansa, kamar yadda gwamna Nasir Elrufa'i ya fadi.
A daren ranar Alhamis ne dai aka sace 'yan matan an makarantar kwana ta Engravers College da ke kusa da birnin Kakau Daji a kudancin birnin Kaduna.
Gwamna Nasir Elrufa'i ne ya sanar da haka yayin wani jawabi ga manema labarai da yammacin Juma'a a birnin na Kaduna.
"Sun nemi a ba su kudi kuma ana tattaunawa." In ji Gwamna Nasir Elrufa'i.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya kuma yi magana da daya daga cikin iyayen 'yan matan da aka sace.
"'Yata ta kira ni da duku-dukun ranar Juma'a a waya amma ban san lambar ba."
"Tana kuka cikin yanayin firgici."
Za a iya cewa ba wannan ne karon farko da ake yin garkuwa da 'yan mata 'yan makaranta a arewacin Najeriya ba.
Sai dai masu fashin baki na ganin yanayin sace wadannan 'yan matan ya sha banban da na baya da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi a Chibok da Dapchi.

Comments

Featured Post

Yadda Zaka Chanja Bayananka Na BVN

table of contents title