Main menu

Pages

Direbobin manyan motoci sun rufe hanyar Zaria zuwa Kano

Bayanai da ke fitowa daga garin Kwanar Dangora da ke kan hanyar Zaria zuwa Kano na cewa direbobin manyan motoci sun rufe hanyar ruf, al'amarin da ya janyo tsayawar sufuri a kan hanyar cik.
An dai ce al'amarin ya faru ne bayan da wani soja ya harbe wani direban babbar motar Dangote sakamakon tsayar da shi da suka yi a shingensu amma bai tsaya ba.
To sai dai wani direba mai suna Tasi'u Hassan ya shaida wa BBC cewa "Soja ne ya harbi dan uwanmu a kansa, abin da ya janyo motar ta kwace masa ta buge mutum biyu."
Ya kara da cewa "direban ya umarci yaronsa da ya sauka a Kwanar Dangora domin ya tambaya musu hanyar zuwa garin Rano, kafin ka ce komai sai wani soja ya fidda bindiga ya harba cikin motar inda ya samu direban a kansa."
Yanzu haka an ce matafiya sun yi cirko-cirko a hanyar sakamakon datse hanyar da direbobin suka yi domin nuna fushinsu ga abin da sojojin suka aikata.
Wata mace ta shaida wa BBC cewa "tun karfe daya na rana muke a wurin nan kuma ba su san yaushe za mu samu hanya ba."
Direbobin manyan motocin dai sun ce ba za su bude hanyar ba har sai jami'an gwamnati sun je wurin domin mika musu kokensu.
Wannan dai kusan shi ne karo na biyu a baya-bayan nan da matafiya a kan hanyar kan fuskanci irin wannan tsaiko.
A jajiberin babban sallah, irin haka ta faru inda direbobin manyan motocin suka rufe hanyar Abuja zuwa Kaduna sakamakon harbe musu dan uwa da wani dan sanda ya yi.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir ne ya yayyafa wa wutar rikicin ruwa har jama'a suka samu suka isa wuraren da suka nufa.
Jami'an tsaro dai na yawan zargi direbobin manyan motoci da yi musu cin fuska a kan titunan kasar.

Comments

Featured Post

Yadda Zaka Chanja Bayananka Na BVN

table of contents title