Main menu

Pages

Batun yawan kudin da ake biyan 'yan fim a masana'antar shirya fina-finan ta arewacin Najeriya ga alama ya raba kan 'yan Kannywood biyu.

 


Tun bayan da BBC Hausa ta wallafa bidiyon hirarta da Hajiya Ladin Cima a filin Daga Bakin Mai Ita, sai ce-ce-ku-ce ya barke kan batun nawa ake biyan jarumai.

Ainihin hirar an yi ta ne ranar Lahadi 14 ga watan Nuwamban 2021, a lokacin da BBC ta aika ma'aikatanta biyu Kano don tattaro shirin Daga Bakin Mai Ita da wasu 'yan Kannywood 11. Amma da yake ana saka shirin daya bayan daya ne a kowace Alhamis, shi ya sa na Ladin Cima bai fito ba sai bayan wata biyu da yin hirar.

Hajiya Ladi da aka fi sani da Tambaya ta Malam Mamman ko Mama Tambaya kamar yadda abokan aikinta ke kiranta, ta shaida wa BBC ne cewa ana biyanta kudin da ba su haura naira dubu biyar ba.

Wannan magana ce ta ja hankalin masu bin shafukan BBC Hausa na intanet inda suka dinga zargin furodusoshi da daraktoci da rashin tausayin tsofaffin 'yan fim din.

Lamarin da ya sosa ran wasu furodusoshin irin su Ali Nuhu da Falalu Dorayi, har suka shaida wa BBC cewa ko su sun taba ba ta kudade masu yawa na fita a fim dinsu da ta yi.

Inda kuma Mama Tambaya ta jaddada wa BBCn cewa an yi haka, bayan sake tuntubarta da muka yi.

Duk da dai Ali Nuhu da aka fi kira da Sarkin Kannywood da kansa ya ce ba za a rasa masu biyan 2,000 ko 5,000 ba, amma bai kamata Ladin Cima ta yi wa duka furodusoshi kudin goro ba.

Wannan hira dai ta zama tamkar bude kofa ne ga wasu abubuwa da suka dade suna ci wa wasu 'yan masana'antar tuwo a kwarya.

Domin tun daga ranar Alhamis, batun dai da ake ta tattaunawa kenan a shafuka daban-daban.

Su ma sauran al'umma ba a bar su a baya ba don sun shiga zancen dumu-dumu tare da bijiro da tambayoyi kan abubuwa da dama da suka shafi Kannywood.

Girma da habaka irin ta masana'antar Kannywood a wannan zamanin, ta wajen nishadantar da al'umma da samar da ayyukan yi da kudaden shiga ga hukumomi, ya sa bai zama abin mamaki ba don wannan batu ya ja hankalin mutane.

Manyan jarumai irin su Nafisa Abdullahi da Nuhu Abdullahi da Hadiza Gabon da Rukayya Dawayya da Tijjani Asase duk sun dan yi gugar zana a shafukansu na sada zumunta.

Wasu kuwa irin su Adam Zango da Rahama Sadau sai suka nuna alamar bakinsu da goro, wato sun dinke shi duk da dai akwai magana.

Wasu na ganin abin da Hajiya Tambaya ta fada gaskiya ne, wasu na ganin ba ta yi daidai ba yayin da wasu kuma ke nuna babu ruwansu kawai dai suna kallon abin da ke faruwa.

Comments

Featured Post

Yadda Zaka Chanja Bayananka Na BVN

table of contents title