Main menu

Pages

Sabuwar Fasaha: Yadda Za'a Iya Maganin KIDNAPPING Da Satar Mutane Daga Wayoyin Hannun Mu (Android) 2019

Da yawan mutane suna siyan wayoyin hannu ne ba don abunda wayoyin suka kunsa ba (facilities) sai don ado ko burgewa.

Wani har ya jima da wayar tasa baya iya sanin wata bukata ta musamman da wayar zata iya yi masa a al'amuran sa na yau da gobe. Waya ta shafi dukkan wani bangare na rayuwar dan Adam har da tsaron rayuka da gujewa fadawa hadari kamar kidnapping. Da yawan mutane suna amfani da applications na wayoyin su amma basu gama kewayewa da abubuwan da wannan applications zasu amfane su ba.


Wani zai iya tambayar kansa ta yaya zan iya maganin kidnapping ko satar mutum ta hanyar amfani da wayar hannu?


Wannan abu ne mai sauki kuma mai saukin ganewa. A yanzu mafi yawan masu amfani da wayoyi suna yin whatsapp.

 Ta hanyar amfani da whatsapp zaka iya maganin kidnapping ko da anyi kidnapping naka za'a iya gane a inda kake cikin sauki. Yadda zaka yi hakan shine:


1. Ka kunna "location" na wayar ka.


2. Ka shiga whatsapp application ka zabi wanda kake so ka yiwa sharing location din.
Saika shiga nan 👇


3. A kasa, inda kake sharing hotuna zaka ga option na "location"
Sai ka shiga zaka ga yana detecting current location din kake a wannan lokacin.
Bayan ya gama zai nuna maka unguwar da kake a map.
Daga nan kana da zabi guda biyu. Zaka iya sending current location din da kake ko kuma kayi sharing live location.

Banbancin na farko da na biyun shine:
Sending current location: shine ka turawa wani inda kake a wannan Lokaci.

Wannan zai taimaka idan aka kama mutum baa san inda yake ba. Idan ya turawa wani location din za'a gane wajen da yake ba tare da shan wahala ba.

Comments

Featured Post

Yadda Zaka Chanja Bayananka Na BVN

table of contents title