Main menu

Pages

Malamin addinin Musulunci Sheikh Abdallah Usman Godon Kaya ya janye ikirarin da ya yi kan ma'aikatan lafiya

Cikin wani jawabi da ya yi da aka gani a wani bidiyo, malamin addinin Musuluncin ya zargi ma'aikatan lafiyan da mu'amular da ba ta dace ba, ciki har da zina da cin zarafin mata. Tun da farko jaridar intanet ta Sahelian Times ta ruwaito shehin malamin yana zargin ma'aikatan lafiya da aikata zina yayin wani shirin talabijin da aka haska a tashar talabijin ta Africa TV mai zaman kanta. Sai dai daga baya ta ce baya malamin ya janye kalaman nasa, bayan da ƙungiyar ma'aikatan jinyan ta ce kalaman nasa ɓata wa ƴaƴanta suna ne, tare da neman ya janye su. Ga abin da ya shaida wa BBC baya da aka tuntuɓe shi kan kalaman nasa. Ya gaya wa BBC cikin wani sakon murya da ya aika cewa "Ban yi niyyar cutar da kowa ba, kuma ya kamata mutane su zama masu kyautata tunanin alheri." Sheikh Gadon Kaya ya shaida wa BBC cewa wasu ma'aikatan lafiya ne suka fara tuntuɓarsa kan wannan lamarin da ke ci gaba da jan hankalin jama'a. "Wasu ma'aikatan kiwon lafiya biyu, namiji da mace ne suka kira ni, muna karatu ne suka yi min fatawa, inda suka fadi matsalar da suke fuskanta ta haɗa mace da namiji, wani lokacin a cikin aiki na dare. "Suka koka, kuma na yi bayani a matsayina na almajiri, mai nusantar da mutane akan aikata daidai." Ya ce ya yi bayani ne cewa matukar hakan na faruwa ya kamata a gyara: "Ya kamata a tsare mutunci matan nan da iyalanmu da 'ya'yanmu gaba ɗaya." Sheikh Gadon Kaya ya ce bayan da kalaman nasa suka tayar da hankalin jama'a, musamman ma'ikatan lafiya, ya zauna da su, inda ya ce "sun warware min dukkan abubuwan da suka shige min duhu kan wannan lamarin." Ya ce ma'aikatan lafiyan sun "yi gungu kuma sun ziyarce ni". Ya kuma ce sun sanar da shi cewa labarin da ya yada babu ƙamshin gaskiya cikinsa, kuma ya ce ya hujjarsa ita ce "wasu ma'aikatanku ne suka kira ni, suka tambaye ni a karatu kuma na bayar da jawabi, inda na ce a gyara". "Laifina shi ne na ce idan wannan abin yana faruwa, na ce a gyara." Ya ce bayan da suka "yi min bayani, kuma na yi musu bayani, mun fahimci juna. Sai na ce mu su 'ba ku fahimci maganganun da ake yadawa ne ba'." Ya kuma yi karin bayani, inda yace dalilinsa na biyu na furta wadannan kalaman masu tayar da hankali shi ne domin yana cikin masu yin kira ga al'umma da a rungumi karatun kiwon lafiya domin saboda akwai bukatar su cikin al'ummar kasar. Shehin ya ce bayanan da ma'aikatan lafiya suka yi kan batun, ya ƙaru da wasu abubuwan da a baya bai sani ba. Sai dai ya kare kansa inda ya ce bai ambaci sunan inda matar da ta yi masa tambayar ta fito ba. "Ban san daga wace jiha tambayar ta fito ba kuma ban ambaci sunan wata jiha ba, ballantana wasu suce da su nake wannan maganar." 'Babu gaskiya kan kalaman Mallam Gadon Kaya' Tun da farko shugaban ƙungiyar ma'aikatan lafiya na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Maikarfi Muhamad ya mayar da martani bayan da kalaman na Sheikh Gadon Gaya suka bayyana. Yayin wata hira da ya yi da mujallar Jarida Radio ta intanet, ya yi kira ga malamin addinin Islaman da ya gaggauta janye kalaman nasa, wanda ya ce na ɓatanci ne. "Cikin maganganunsa yana cewa ma'aikatan lafiya suna kwana a daki daya, har yana hasashe cewa wani mummunan abu yana faruwa tsakaninsu, inda ya kawo misalin wata mata mai shekara 50 da haihuwa kuma ya yi kwatanci kan wasu matasa 'yan matan da shekarunsu ba su kai 30 ba cewa suna kwana a daki daya, a bisa teburi daya a wurin da suke aiki na kwana." Kwamared Muhammad ya yi kira ga ma'aikatan lafiya da su kwantar da hankalinsu kan munanan kalaman da Sheikh Gadon Kaya ya yi amfani da su, wadanda ya ce suna iya ɓata musu suna. "Muna gaggauta jan hankalin wannan malami da ya yi hanzarin janye wadannan kalaman da ya furta ya kuma ba ma'aikatanmu da al'ummar jihar Kano hakuri." Shugaban kungiyar ma'aikatan lafiyan ya ce kalaman na iya tayar da hankalin magidantan da matansu ke tafiya aikin asibiti da dare. Ya kammala jawabin nasa da yin kira ga malamin addinin da ya gaggauta janye kalaman ko kuma su dauki matakin shari'a a kansa. Sharhi daga Sani Aliyu, BBC Hausa Wannan batu dai ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a Najeriya musamman daga masu amfani da shafukan sada zumunta. Mutane da dama na tsokaci da batun masu iya magana da ke cewa: "Iya ruwa fid da kai," kuma "Baki shi kan yanka wuya". Wadannan karin maganar biyu sun shafi kowane fanni na zamantakewa da na rayuwar al'umma, musamman ma a bangaren da ya shafi addini. Malaman addinin a Najeriya na da karfin fada a ji, musamman ganin yadda 'yan kasar ke bin dukkan kalaman da suke furtawa sau da kafa. Lamarin bai tsaya kan malaman addinin Musulunci ko na Kirista ba, domin dukkan mabiya manyan addinan biyu na wa malamansu biyayya. Wannan ne yasa dukkan abin da suka fada ke jan hankulan jama'arsu sosai kuma kalaman ke yin tasiri kan yadda mabiyansu ke kallon batutuwan da malaman ke yin tsokaci akai. Wannan takaddamar da ke tsakanin Sheikh Abdallah Gadon Kaya da ma'aikatan kiwon lafiya misali ne na irin wadannan batutuwan da ya dace malamai su rika yin tsantseni akai gabanin bayyana wata matsaya, kuma ba wannan ne karo na farko da kalaman nasa ke tayar da hankulan al'ummar da yake ikirarin nusantarwa daga aikata laifuka ba. Idan ba a manta ba, a bara Sheikh Abdallah Gadon Kaya ya taba furta kalaman da wasu ke kallo a matsayin na ɓatanci, kuma wadanda ka iya taɓa mutuncin babban limamin masallanci kasa da ke Abuja, wato Sheikh Ibrahim Maqari. Sai dai rahotanni sun ce an shiga tsakani kafin aka kashe wutar rikicin da ta rika ruruwa bayan da kalaman Sheikh Gadon Kaya suka bayyana, inda daga baya Sheikh Gadon Kayan ya nemi afuwa daga Sheikh Maqari, amma sai bayan da ya shigar da ƙara a kotu a watan Agustan 2021. Kuma da alama, kamar sauran al'umma, malaman addinai ma na amfani da kafofin sada zumunta wajen yaɗa ra'ayinsu kan batutuwan da suka shafi rayukan 'yan kasa. Sauƙin hawa wannan mumbari na intanet ko na sada zumunta ya haifar da dubban masana kan kowane fanni na rayuwa, ciki har da na addinai. Sai dai a wasu lokutan, mutane da dama na ganin wasu malaman kan bayyana ra'ayinsu ne ba tare da sun yi cikakken bincike ba, kuma wasunsu ba sa tauna tasirin kalamansu kan al'umomin da suke yi wa jagoranci ta bangaren addini. Wannan ne yasa masu sharhi ke ganin yake da muhimmanci jagororin al'umma - musamman ma malaman addinai - su rika cizawa kuma suna hurawa kafin su yi sharhi kan kowane batu.

Comments

Featured Post

Yadda Zaka Chanja Bayananka Na BVN

table of contents title