Kamfanin Samsung ya daukaka kara domin kalubalantar kudaden da kotu ta umurci ya biya kamfanin Apple da ke zargin an kwaikwayi fasaharsa.
Tun 2012 Kotu ta bukaci Samsung ya biya Apple dala miliyan $548 na diyya.
Apple ya kalubalanci Samsung ne da kwaikwayar kirar wayoyin shi na Salula, yanzu kuma Samsung ya daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.
Apple dai kamfanin Amurka ne, amma Samsung na mallakin ‘Yan Korea ta kudu ne da ke samun kasuwa a Amurka da Turai da Afrika.
Apple ya kalubalanci Samsung ne tun fito da wayoyinsa kirar Galaxy.
Comments
Post a Comment