Main menu

Pages

Yadda zaka sayi 200mb a Naira 50 kacal a Layin MTN

Masu bibiyar wannan shafi barkan mu da wannan lokaci kamar dai yadda muka daba duk lokacin da wata garabasa ta samu muna zo muku da bayani a kai domin kowa ya amfana,
Sabo da haka a yanzu ma nazo muku ne da takaitaccen bayani game da yadda ake siye damen shiga tanar gizo 200mb akan kudi Naira 50 kacal a layin MTN.
Ba tare da bata lokaci ba ga yadda abun yake,
Farko zaka saka kati a layin ka na MTN sai ka danna wadannan lambobi *131*25# zas baka zabi biyu na farko idan kana bukatar a duk lokacin da kwanaki 7 ya cika su sake dinar Naira 50 su baka wani to sai ka danna lamba 1 idan kuma baka bukata sai ka danna lamba 2 nan take zasu debi Naira 50 su baka 200mb na tsawon kwanaki 7,
Sai dai ba ko wane layi yakeyi ba domin nima na gwada a layuka 2 basuyi ba sai na nayi nasara yayi.
Dan haka yana da kyau tun kafin ka saka kudi ka gwada danna wadannan lambobin *131*25# idan layin ka yana yi zaka gani idan kuma baya yi zasu turo maka sako kamar haka.
Y'ello! You are not eligible for this offer. Please dial *131*1# to buy other data bundles. Thank you.
Allah ya bada sa'a.

Comments

1 comment
Post a Comment

Post a Comment

Featured Post

Yadda Zaka Chanja Bayananka Na BVN

table of contents title